Garin Aliero dake cikin karamar hukumar Aliero, cibiyar noman albasa ne a jihar Kebbi, gida ne ga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi (KSUSTA). Jami’ar wacce ke da nisan kilomita 46.5 daga babban birnin jihar, Birnin Kebbi, an kafa ta ne a watan Disambar shekarar 2006 ta hanyar dokar jihar Kebbi A doka mai lamba 6. Wannan shiri ya samo asali ne daga bukatar jami’a a jihar da za ta dauki nauyin ’yan asalin jihar da suka cancanta da ba za su iya shiga jami’o’in Najeriya ba saboda karancin gurabe. Ta samu lasisin zama jami’a ta 79 a Najeriya, tun lokacin da aka fara karatu a watan Janairun 2008 tare da dalibai 404, KSUSTA ta samu karuwar dalibai 8,813 da suka hada da dalibai 8,466 da suke karatun digiri na farko da 347 da suke karatun gaba da digirin farko.
Duk da fadada da sassan ilmi daban daban suka samu a jami’ar, sashen noma na jami’ar ya daɗe yana kokawa a kan rashin muhimmin dakin bincike da sarrafa aikin noma na zamani (greenhouse).
Mataimakin shugaban jami’ar wanda ya gabata Farfesa Bashir Ladan Aliero, ya yi tsokaci kan gaggawar samar da wannan wurin binciken, inda ya jaddada cewa, dakin bincike na greenhouse zai inganta ingancin koyarwa da kuma bada damar bincike. “Wannan gidan na shirin zama muhimmiyar kadara wajen inganta karatun noma na jami’ar da kuma aikin bincike, wanda zai amfanar da sauran al’umma manoma,” in ji shi.
Shekaru da yawa, rashin wurin bincike na zamani waton greenhouse ya tilasta wa masu binciken jami’ar su mayar da gwaje-gwajen su zuwa gonar lambu, wanda ke iyakance ikon su na gudanar da nazarin da sarrafa aikin gona. Mataimakin shugaban jami’a ( na Gudanarwa) kuma shugaban sashen aikin gona, Farfesa Musa Augie, ya lura cewa wannan kalubale na rashin wurin bincike ya hana gudanar da bincike mai mahimmanci game da canjin yanayi, juriyar shuka a gona da lafiyar ƙasa. Idan ba tare da wannan wurin bincike da sarrafawa ba, nazari kan juriya da cututtuka da ayyukan noma na zamani bazasu yiwu ba. Sakamakon haka, ɗaliban aikin noma da ilmin halittu sun rasa damar yin amfani da wannan wurin mai mahimmanci, tare da rage ƙwarewarsu wurin samun aikin yi a aikin noman zamani.
Jami’ar ta kara fuskantar kalubable a cikin Nuwamba 2023 lokacin da ƙungiyar masu ba da izini ta ziyarci KSUSTA kuma ta nuna damuwa game da rashin wurin bincike da sarrafawa na zamani (greenhouse) a makarantar. Farfesa Maikasuwa, Mataimakin Shugaban Jami’ar (Academic), ya ce, “Ba za ku iya samun sahihin bangaren koyar da sashen noma ba ba tare da dakin bincike da sarrafa aikin noma na zamani ba .” Bukatar neman mafita ya fito fili daga bayanansa.
Bisa la’akari da muhimmiyar rawar da dakin bincike da sarrafa aikin noma na zamani ke takawa wajen bincike da ilimi a fannin noma, shirin Hukumar Ƙarfafa juriyar sauyin yanayi da aikin noma a yankuna masu karancin ruwan sama (ACReSAL), wani shiri na bankin duniya (World Bank) ta hannun ofishin gudanarwa na jihar Kebbi (Kebbi State Project Management Unit – SPMU) ya dauki matakin samar da wani katafaren dakin bincike da sarrafa aikin noma na zamani a KSUSTA. An fara aikin ne a watan Satumba na 2024. A cewar Mataimkin Shugaban Jami’ar (DVC), an gina shi don zama daya daga cikin mafi girma kuma na zamani a wuraren samar wurin bincike da sarrafa aikin noma a fadin jami’o’i a Najeriya.
Yayin da aikin gina ya kusa kai karshe, tasirinsa ya riga ya bayyana. Sabon wurin binciken zai ba da damar gwaje-gwajen aikin gona na shekara zuwa shekara, ba da damar masu bincike da ɗalibai su yi nazarin daidaita yanayin gona, kara jure yanayi na shuka, da magance kwari. Horar da dabarun noma na zamani zai ba wa ɗalibai ƙwararrun sana’o’in hannu, da haɓaka aikin yi da kuma ba da gudummawa ga aikin noma mai dorewa. Bugu da kari, wurin binciken zai samar da damammaki don samar da kudaden shiga ta hanyar samar da damar sayar da tsirrai da kayan marmari, da tallafawa ci gaba da bincike da ayyukan da dalibai ke jagoranta, wanda Babban Jami’in Ayyukan Jiha (SPC), Ahmad Isa-Tela, ya bayyana.
Dorewar wannan aiki yana cikin abinda aka ba himma. KSUSTA na da burin karfafa hadin gwiwa da sauran cibiyoyi da ma’aikatar noma da albarkatun kasa ta jihar Kebbi domin tabbatar da amfani da wurin yadda ya kamata. Farfesa Saadu Umar, DVC Research and Innovation, ya jaddada cewa jami’ar tana da Kwararru da ƙwarewar fasaha don sarrafawa da kuma ci gaba da gudanar da wurin binciken yadda ya kamata.
Aikin ACReSAL ya yi hasashen wannan yunƙurin a matsayin wani tsani don haɓaka bincike, ilimi, da dorewar noma. A cikin al’ummar da ke fafutukar samar da abinci, ayyukan tallafa wa hukumomi/jami’o’i kamar kafa wannan wurin binciken zai taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa bincike da samar da abinci, wanda zai sa Najeriya ta zama mai juriya wurin ciyar da kanta.
Daga karshe, kafuwar wannan wurin bincike da sarrafa aikin noma na zamani a KSUSTA yana nuna gagarumin ci gaba a ilimin aikin gona da bincike ya samu a jihar Kebbi. Zaya kafa jami’ar a kan turba mai kyau a fannin aikin gona, kimiyyar muhalli, da tabbatar da cewa bincike da kirkire-kirkire suna bunƙasa yayin da suke ba da gudummawar samar da abinci, kiyaye rayayyun halittu, da juriyar yanayi. Wurin binciken ba wurin aiki ba ne kawai; kofa ce ta ilimi, kirkire-kirkire, da kuma makoma mai dorewa ga fannin noma a Najeriya.
ACReSAL!
“… raya muhalli, ceto rayuwa”
Hotuna














